Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar APC A Jihar Nasarawa Na Kokarin Hada Kan 'Yan Jam'iyyar Biyo Bayan Zaben Fidda Gwani


Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Nasarawa sun yi wani zama na musamman da ‘yan takara da suka fafata a zaben fidda gwani don dinke duk wata Baraka da ka iya kunno kai a jam’iyyar.

Mutane goma sha daya ne suka tsaya neman takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, yayinda mutane bakwai suka tsaya yin takarar sanata, sai mutane ishirin da tara suka yi takarar majalisar wakilai, mutane dari da goma sha bakwai kuma suka tsaya takarar ‘yan majalisar jihar ta Nasarawa.

Sakataren jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, Aliyu Bello yace makasudin taron shine don su kira wadanda basu sami nasara a zaben fidda gwanin ba don su goya baya ga wadanda suka yi nasara don cimma burin jam’iyyarsu.

Ita ma Onarabul Mary Enwongulu, wacce ta tsaya takarar sanata amma bata yi nasara ba, tace ta hakura kuma zata goyi bayan wanda yayi nasara.

Shiko Gwamnan jihar ta Nasarawa, Umaru Tanko Almakura yace taron yayi tasiri don duk ‘yan takarar da suka fadi zaben sun rungumi kaddara da alkawarin zasu yi wa jam’iyyar aiki har ta kai ga nasara a zabe mai zuwa na shekarar mai zuwa da ake shirin yi.

Ga Zainab Babaji da rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG