Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyu Na Shirin Fafatawa a Zaben Gwamna a Fadin Najeriya


INEC

Duk da ya ke an gama da zaben shugaban kasar Najeriya, har yanzu fagen siyasar Najeriya na tsuma. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da muhimmancin da ake bai wa zaben gwamnonin jahohi ba. Tuni dai APC da PDP su ka fara karce kasa don shirin bugawa musamman a wasu jahohin.

Ga dukkan alamu za a fafata matuka a zaben gwamnonin jahohin Najeriya da ke tafe ranar Asabar, saboda kowacce daga cikin manyan jam’iyyun nan biyu, da ma wasu da ke biye da su, ta dukufa ba ji ba gani wajen ganin cewa ta kai labari.

Duk da rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta yi, wannan bai hana ta daura damarar gwabzawa a zaben gwamnonin jahohi ba. Hasali ma, jam’iyyar ta PDP ta cigaba da amfani da kalaman da ta yi amfani da su a yakin neman zaben shugaban kasa. Alal misali, Sakataren jam’iyyar ta PDP, Alhaji Umar tsauri, ya sake zargin cibayan tattalin arziki da wanzuwar kuncin rayuwa da tabarbarewar tsaro da rashin ayyukan yi da kuma shaye-shaye tsakanin matasa wai saboda takaici.

Su kuwa a nasu bangaren, ‘yan APC sun ce an yi kaca-kaca da Najeriya gabanin hawarsu mulki ta yadda sai da su ka yi da gaske kafin abubuwa su ka fara daidaita. Sakataren APC Mai Mala Boni ya ce don haka jam’iyyar APC ta himmantu ga kare nasarar da ta yi saboda kar PDP ta mayar da hannun agogo baya a matakin jahohi.

Sauran jam’iyyu ma irinsu PRP sun ce lalla za a dama da su a zaben gwamnonin. Dan takarar gwamnan jahar Bauchi karkashin PRP Furfesa Ali Pate ya yi zargin cewa ana wani abu shigin kama karya a siyasar kasar. Y ace da bukatar a yi koyi da salon siyasarsu.

Ga Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG