Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a mu Kai Kukan mu ga Allah


Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa
Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Yayin da wasu jama’a ke zanga-zanga akan rashin gamsuwa da matakin da ‘yan majalisa jihar Nasarawa suka dauka na tsige gwamnan jihar Umaru Tanko Almakura, wasu cewa suke matakin yayi dai dai.

A yau wasu magoya bayan gwamnan suka gudanar da zanga-zangar lumana inda suka isa fadan sarkin lafiya Mustapha Isa Agwai domin nuna takaicinsu kan matakin da ‘yan majalisa suka dauka.

Masu zanga- zanga sunce idan ‘yan majalisa nayi don taklakawa ne to su dakatar dashi domin a cewar su gwamna yayi rawar gani a birni da kauye.

Shi kuwa sarkin na Lafiya, kira yayi ga alumna jihar Nasarawa dasu kwantar da hankulansu, sailin nan ya umarcesu dasu kai kukansu ga Allah.

A bangare daya magoya bayan ‘yan majalisan sun ce suma zasu gudanar da nasu zanga-zangar akan ci gaban da aka samu a jihar domin ‘yan majalisa suna yin aiki daidai da abun da suke so.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG