Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Na Kara Kira A Binciki Patience Jonathan, Matar Tsohon Shugaban Najeriya


Patience Jonathan matar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Patience Jonathan matar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Biyo bayan karar da Patience Jonathan ta shigar a kotu tana neman a sake mata wasu miliyoyin dalar Amurka da aka gano a bankin Sky, ya sa jama'a na kara kiran a gudanar da bincike a kanta

Tun can farko hukumar EFCC ta rike wasu kamfanonin Patience Jonathan hudu da su ma tana neman a sake mata.

Da ma can ita EFCC din na binciken wani hadimin cikin gidan tsohon shugaban wato Mr. Dudafa da badakar miliyoyin dalar Amurka da ya kai ga rufe ma'adanin bankin. Hakan ya sanya Patience Jonathan fitowa fili ta nuna cewa wadannan kudaden nata ne.

Bugu da kari Patience ta ma kai bankin Sky kara domin neman bin kadin kudin.

Kungiyar tabbatar da adalci ga lamuran zamantakewa da tattalin arziki, SERAF, a takaice, ta bada wa'adin kwana bakwai ga ministan shari'a Abubakar Malami ya gurfanar da Patience Jonathan gaban kotu ko kuma kungiyar da dauki matakin shari'a da zai nemi tilasta binciken Patience.

Wani rahoton bayan fage na nuna neman tunkarar gwamnatin Buhari da batu sako kudin na Patience amma wasu jami'an gwamnati suka nuna cewa batun na EFCC ne kuma gwamnatin Buhari bata sa baki a harkokin hukumar.

Kwamred Abubakar Abdulsalam, shugaban wata kungiya dake yaki da cin hanci da rashawa dake mara baya ga matsayin na SERAF yace an dade ana ganin kamar matar shugaban kasa ko gwamna na cikin tsarin mulkin Najeriya amma kuma babu wannan a tsarin mulkin kasar. Duk da haka duk wani tsarin mulkin kasar sai ka ga matan suna da ruwa da tsaki ciki, suna harka da dukiyar jama'a da aiwatar da mulki kamar dokar kasa ce ta basu.

Yace daidai ne wa'adin kwana bakawai da aka ba ministan shari'a idan kuma bai yi haka ba ya nuna ba dagaske suke ba akan yaki da cin hanci da rashawa. Idan da gaske ne ba za'a kama wannan a bar wancan ba. Kowa aka samu da laifi a taboshi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG