Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'atul Nasril Islam, JNI Ta Kira a Zauna Lafiya Kada a Dauki Fansa


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar kuma shugaban Jama'atul Nasril Islam, JNI a duk fadin Najeriya
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar kuma shugaban Jama'atul Nasril Islam, JNI a duk fadin Najeriya

Biyo bayan harin da aka kaiwa 'yan arewa a kudu maso gabashin Najjeriya ya sa shugabannin arewa musamman na Jama'atul Nasril Islam suke ta kiran jama'arsu kada su dauki fansa kan yan kudu dake zaune a arewa.

Fargabar daukan fansa ta sa shugabanni a duk arwacin Najeriya na ta kiran al'umma kada a dauki matakin fansa a rewacin kasar.

Kungiyar Musulmin Najeriya ta Jama'atul Nasril Islam, JNI, na cewa ya zama wajibi a kira al'umma kada wanda ya dauki fansa.

Sakataren kungiyar ta JNI Dr Kari Aliyu Abubakar shi ya yiwa manema labarai karin haske. Yana mai cewa a matsayinsu na shugabannin addimi suna kira a kai hankali nesa. Sun yi anfani da masallatai sun kira a yi huduba kan zaman lafiya yau a kwantar da hankulan mutane musamman matasa tunda gwamnati ta ce za ta dauki matakai.

Ita ma kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya ta ce ta gamsu cewa an fara samun zaman lumana a kudancin kasar. Ta kira doka ta yi aikinta akan duk wadanda suka tada hayaniya.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG