WASHINGTON, DC —
Jami’an Ghana sunce babu wani dan wasan kasar da yayi tawaye a gasar cin kofin duniya.
Larabannan ne Jami’an harkokin wasannin kungiyar kwallon kafar kasar Ghana suka karyata jita-jitar dake yaduwa mai cewa wasu ‘yan wasa sunyi wa Kwach Kwesi Appiah tawaye, biyo bayan cinyewar da kungiyar Amurka tayi musu na 2-1 a baya-bayannan.
Wani gidan Radiya a Ghana mai suna Joy FM yace ‘yan wasa musamman ma wanda yake doka kwallo a Jamus, Kevin-Prince Boateng ya nuna bacin ranshi da hikimar kwach Appiah, a lokacin da suka sha kashi a hannun Amurka. Boateng da Micheal Essien wanda yake bugawa kungiyar AC Milan sun sha benci a farkon wasan dake karkashin rukunin Group G.
Muna so mu tabbatar cewa rahotannin dake zagayawa ba gaskiya bane, kuma basu da tushe balle makama, inji Hukumar Kwallon Kafar Ghana. “Babu wani dan wasa da yayi tawaye, biyo bayan faduwar da kungiyar mu tayi a hannun Amurka inda aka cimu 2-1.