Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Gwamnatin Nijar Sun Fantsama cIkin Jihohi Takwas Saboda Rashin Damina Mai Kyau


Ministan Man Fetur na Jamhuriyar Nijar, Fumukwai Gado yana ziyara a jihar Tawa
Ministan Man Fetur na Jamhuriyar Nijar, Fumukwai Gado yana ziyara a jihar Tawa

A jamhuriyar Nijar jami'an gwamnati ne suka fantsama cikin jihohi takawas saboda rashin damina mai kyau a wasu sassasn kasar da zummar shirya yadda za'a taimakesu da cimaka

Karshen daminar bana bai zo wa wasu jihohi da kayu ba lamarin da ya haddasa karancin cimaka na mutane da na dabbobi.

Ministan Man Fetur na kasar Malam Fumukwai Gado ya soma tashi ziyarar a birnnin Konni dake jihar Tawa. Yace sun kawo ziyarar ne domin su ga sakamakon daminar bana a yankin. Yace a fannin cimaka kamar rahoton da aka bashi a gidan gona an samu raguwa bisa ga na bara.

A jihar yace sun gano akwai garuruwa 63 da zasu samu karancin cimaka. A wani yankin ma akwai garuruwa 39 da zasu samu matsalar cimaka. Saboda haka tun yanzu a soma daukan matakan da za'a samar wa masu noman rani domin a rage matsalar karancin cimakan na mutane da dabbobi.

Dangane da abincin dabbobi za'a samu ragowar kashi hamsin bisa ga na bara. Dole ne gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa.

Ministan kuma ya tattauna da makiyaya da manoma saboda hatsaniyar da aka samu tsakaninsu.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG