Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Hukumar Agajin NEMA Sun Fara Yajin Aiki


Ma'aikatan hukumar bada agajin jinkai ta Najeriya sun koka akan rashin biya masu bukataunsu da gwamnati ta yi.

Jami’an hukumar agajin gaggawa ta NEMA sun fara yajin aikin gargadi na wuni uku da kuma neman shugaban hukumar Injiniya Mustapha Mai Jaja yayi murabus.

A yau Alhamis jami’an sun yi wani gangami a gaban shelkwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja, dauke da kwalayen bukatar a sauke Injiniya Mai Haja daga mukaminsa, ba ma akan batun matsin lambar cimma muradan alawus da kayan aiki ga jami’an ba.

A nasa bangaren Injiniya Mai Haj ya ce tirjiyar ma’aikatan ta zo da bam mamaki. Ya ce gwamnati ta sanyawa wasu bukatun ma’aikatan hannu wasu kuma sai nan gaba.

Mai Haja yayi kira ga ma’aikatan akan su koma bakin aikinsu saboda dole ne a bi ka’idodin gwamnati kafin a biya masu bukatunsu.

Ga karin bayani a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG