Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Kwastan dake Yammacin Najeriya Sun Kama Motoci Shake da Shinkafa


Najeriya

Jami'an kwastan dake kula da jihohin Oyo da Osun a yammacin Najeriya sun kama wasu motoci shake da shinkafa da aka boye ta yin anfani da katakai da shanu.

Jami'an sun kama manyan motoci shake da buhuhuwan shinkafa da katako da kuma manyan shanu.

Abdulsalam Hassan mataimakin kwantrola mai kula da jihohin Osun da Oyo yace sun kama motoci hudu da suke dauke da buhuhuwan shinkafa dari tara. Dukansu cikin jihar Oyo aka kama su.

Masu fasakwaurin shinkafar sun yi anfani da shanu da kuma katako domin batar da sawu, wato kada a ga shinkafar.

Tunda gwamnati ta yadda a shigo da shinkafa a hukumance domin a biya kudin kwastan, ita hukumar kwastan ta hada hannu da wasu da zasu dinga tsegunta mata idan wani ya yi yunkurin shigo da shinkafa ba tare da son biyan kudin kwastan ba.

An kama mutane biyu dangane da batun shinkafara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG