Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro A Syria Sun Bude Wuta Kan Masu Zanga Zanga


Sojojin Syria suke sintiri.

Rahotanni na cewa akalla mutane tara ane suka halaka bayan da jami’an tsaron Syria suka bude wuta a kan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnati.

Rahotanni na cewa akalla mutane tara ane suka halaka bayan da jami’an tsaron Syria suka bude wuta a kan masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria a yau Juma’a.

Shaidun gani da ido suka ce jami’an tsaron Syria sun yi amfani da bindigogin dake dauke da harsasai suka rika harbin masu zanga-zangar a birnin Homs.

A halin da ake ciki, masu zanga-zangar sun ci gaba da gudanar da zanga-zangarsu a kan muhimman titunan biranen kasar Syria.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya jiwo daga bakin wani dan rajin Demokuradiya na cewa masu zanga-zangar suna rike da ganyen itatuwan Zaitun suna kirarin a basu ‘yancinsu.

XS
SM
MD
LG