Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro A jihar Delta Sunce Sun Kame Wasu Mutane Da Ake Tuhuma Da Kai Hari A Jihar.


Jami'an tsaro a wata mazaba a Kano

Jami'an tsaro a jihar Delta sunce sunyi nasarar kame wasu mutane biyu da ake tuhuma da kaiwa wasu mutane hari a Asaba dake cikin jihar Delta.Jami'an suka ce suna nan suna ci gaba da bincike domin zakulo sauran wadanda ake tuhuma da kai wannan harin.

A ‘Yan kwanakin nan ne dai wasu mutane suka kai wa wasu al’umma a birnin Asaba dake jihar Delta farmaki, inda mutane 4 suka rasa rayukkansu, wasu kuma suka jikkata.

Sai dai kuma jami’an tsaron dake yankin kudu-maso-gabashin Nigeria sunce a tsaye suke domin dawo da zaman lafiya a yankin.

DSP Onyemaka Andrew wanda shine kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta ya shaidawa wakilin sashen Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa yanzu haka mutane biyu na hannun su sakamakon harin da aka kai a birnin Asaba dake jihar ta Delta.

Yace ko baya ga kame wadannan mutanen, yanzu haka rundunar tana nan tana ci gaba da bincike, dominzakulo masu hannu cikin wannan danyen aiki.

Ga Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG