Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro na Taimakawa Wasu Kungiyoyi Don Kwato Garuruwan Dake Hannun 'Yan Boko Haram


'Yan Boko Haram.
'Yan Boko Haram.

Kawo yanzu dai rahotanni daga arewacin jihar Adamawa na cewa ‘yan tauri, maharba da jami’an tsaro nafa cigaba da fafatawa da ‘yan bindiga na Boko Haram, kuma ma har an fara kwato wasu yankunan dake hannun ‘yan bindiga masu tada kayar bayan.

Wasu al’umomin yankin summa bayyana cewa baya garin Maiha, yanzu haka fa ‘yan Tauri da Maharban dake samun tallafin sojoji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma tunima suka kutsa yankin Mubi dake hannun ‘yan Boko Haram.

Tuni dai wasu sarakunan da basuyi hijira sun koma Abuja ba, sundai yaba da wannan kokari, mai martaba sarkin Muri a jihar Taraba Alhaji Abbas Tafida yace fa yanzu tura takai bango.

Yan dai ana cigaba da gudanar da addu’o’in Allah ya kawo karshen ‘yan bindiga masu tayarda kayar bayan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG