Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Rivers, Jami'an Tsaro Sun Damke Sakataren Gwamnatin Jihar.


Rivers state, Nigeria
Rivers state, Nigeria

A yayinda ake gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisu ako wani mataki a jihar Rivers, rahotanni sun ce an kama sakataren gwamnatin jihar.

Rahotanni daga jihar Rivers, dake kudu maso kudancin Najeriya, watau yankin Niger Delta, suna nuni da cewa jami'an tsaro sun kama sakataren gwanatin jihar, Mr. Kenneth Kobani. Sai dai har zuwa yanzu ba'a bayyana dalilan da suka sa jami'an soja suka damkeshi ba.

Wasu rahotannin suna nuni da cewa, an samu tashe tashen hankula a wasu kananan hukumomi, da suka hada da Abonima da Bukana a yankin Ogoni.

Wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar Sokkoto, yace a wasu sassa da ya ziyarta a babban birnin kasar Fatakwal, ya lura zaben yana gudana yadda ya kamata kodashike an fuskanci jinkrin kjai kayan zabe a wasu mzabu.

Wasu rahotanni sun ce an kama wata mota da kayan soja na jebu, da kayan aiki na hukumar zabe. Duk da cewa hukumomi basu tabbatar da aukuwar haka kai tsaye ba, sun bada tabbacin suna gudanar da bincike kan haka.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG