Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Kasashen Turai Sun Ce Ba Zasu Yi Sakaci Ba Saboda 'Yan Ta'adda


Shugabannin kasashen Tarayyar Turai

Duk da murkushe kungiyar ISIS a Raqqa da wasu wuraren cikin Syria da Iraq, har yanzu 'yan ta'addan na cikin shirin ci gaba da ta'addanci, daili ke nan da jami'an tsaron nahiyar turai suka ce ba zasu yi sakaci ba

Jami’an yaki da ta’addanci na kasashen Turai sunce ba zasuyi sakaci ba, ganin cewa duk da an kwace ikon birnin Raqqa daga mayakan kungiyar ISIS, har yanzu ‘yan ta’addaci na cikin shiri.

Murkushe kungiyar ISIS da aka yi a babban birnin Syria a farkon watannan, na nuni da yadda ake ta yayata cewa an kawo karshen kungiyar, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya fito, yana bayyana abinamatsayin babbar nasara.

Amma jami’an yaki da ta’addanci sunce akwai alamun cewa kungiyar ISIS ta yadu, musamman ma cikin wani kankanin lokaci.

Babban abin damuwa shine duk kuwa da cewa kungiyar ta rasa ikon wasu muhimman wuraren ta a Syria da Iraq, amma har yanzu kungiyar na samun yin magana da mayakanta dake Turai, da kuma samun neman sabbin mayaka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG