Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Kusar Al-Qa'ida A Tunisiya


Firayim ministan Tunisiya, Youssef Chahed, yana magana da 'yan jarida a lokacin da ya ziyarci wani caji ofis da aka kai ma hari a El Battan, kilomita 35 a yamma da Tunis

Jami'an tsaron kasar Tunisiya na musamman sun kashe wasu manyan mayakan Al-Qa'ida na yankin Maghreb a Tunisia, a yayin da kungiyar ISIS ke daukar alhakin manyan hare haren da aka kai a kasar

A Tunisiya jamia’an tsaro na musamman a kasar, sun kashe wani babban dan Al-Qa'ida a yankin Maghreb, a wani kauye can a wajajen yammacin kasar kusa da iyaka da Aljeriya.

Jami'an kasar sun ce wanda aka kashen shi ne Belal Kobi, wani hadimin babban shugaban kungiyar, Abu Musab Abdul Wadud.

Haka nan an kashe wani dan bindiga a wani matakin soji inda sojoji da dogarawan kasar suka zagaye 'yan wata kungiyar ‘yan ta’adda a yankin Kasserine na yammacin kasar da daren Asabar, a cewar Ma’aikar Harkokin Cikin Gida.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kusan duk manya-manyan hare-haren da ake kaiwa a Tunisiya ciki harda wanda aka kaiwa wani otel da kuma wani wajen adana kayan tarihi da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan yawon bude ido da dama a shekarar 2015, da kuma hare-haren da mayaka dake shigowa daga Libya suka kai a shekarar 2016.

Fiye da 'yan kasar Tunisiya 3000 ne suka bar kasar a shekarun baya bayan nan suka shiga sahun mayakan ISIS da ke Iraq, da Syria da ma Libya. Jami'ai suna kokarin shiryawa domin tunkarar barazanar da kasar zata fuskanta a dalilin komawarsu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG