Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an ‘Yan Sanda Na Kukan Rashin Biyansu Albashin Wata Da Watanni


Babban Sifeton 'Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris
Babban Sifeton 'Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris

‘Yan sanda na kokawa saboda rashin biyansu albashi da alawus har ma wani cikinsu dake Dapchi a jihar Yobe ya koka da irin halin da suke ciki, amma da korafin ya kai kunnuwan babban sifetonsu ya fusata saboda laifin na ma’aikatar kudi ne kuma ya yi barazanar kai kara wurin shugaban kasa idan ba’a biya jami’ansa ba

Yayinda jami’an ‘yan sanda ke fama da rashin samun albashi, daya daga cikinsu da yake Dapchi a jihar Yobe ya bara saboda ya bugawa Muryar Amurka waya ya bayyana halin da suke ciki.

Jami’in da ya nemi a sakaya sunansa yace rashin samun albashi da alawus na Nera dubu daya kowace rana da ya kamata a biyasu saboda inda suke aiki, wato wajejen ‘yan ta’addan Boko Haram, ka iya haddasa koma baya ga aikin tsaro.

A cewar jami’in alawus dinsu na tun watan daya babu wanda ya samu ko kwandala kama daga su dake jihar Yobe har zuwa wadanda suke jihar Borno. Wasunsu sun yi wata uku, hudu ba’a biyasu albashi ba. Suna fama da rashin kudin biyan bukatun iyalansu da ma na yau da kullum. Ya kira gwamnati ta tuna dasu ta yi masu adalci.

Maganar ta kai ga kunne babban sifeton ‘yan sandan Ibrahim Idris wanda ya ba jami’in kula da kudi na rundunar ‘yan sanda ya binciki dalilin dake sa albashin ‘yan sanda ke makalewa a ofishin akantan Najeriya cikin sabon tsarin biyan albashi.

Bala Ibrahim mai taimakawa babban sifeton ya ce a gayawa kakakin rundunar ‘yan sanda cewa matsalar ba a wurinsu take ba. Matsala ce da take da asali a ma’aikatar kudi. Malam Bala Ibrahim ya ce ba dede ba ne a tura mutum daji wurin aiki yana shan rana amma kuma aki biyansa hakkinsa.

A cewar Bala, babban sifeton ‘yan sandan ya yi barazanar kai kara wurin shugaban kasa muddin ma’aikatar kudi bata biya jami’ansa ba. Ya tura jami’insa mai kula da harkokin kudi ya tare a ma’aikatar kudi ta san yadda zata biya jami’ansa.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG