Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Amurka dake Yola ta kafa makarantar yara mata tare da ciyar dasu - 3' 22"


Some IDPS children attending the school

Jami’ar Amurka a Najeriya dake Yola fadar jihar Adamawa tare da hadin gwiwar ofishin jakadanci na kasar Ireland ta kafa makarantar karatu da ciyarwa ga yara mata ‘yan gudun hijira da marasa galihu inda yara mata saba’in ke cin gajiyarta.

Shugabar aiwatar da shirin Malama Turai A .Kadiri ta ce makasudin shirin shine ta ga ta fadada makarantar almajiranta na karatu da ciyarwa ya isa ga yara mata musamman ‘yan gudun hijra da yaran matalauta da yake ba safai ake samun ‘ya mace na almajiranci ba.

Shugabar jami’ra Amurka a Najeriya Dr, Margee Ensign wadda da ta kirkiro shirin ta ce manhajar karatu na shiri ta na karatu da ciyarwa daya yake da na sashin ilimin firamarenta. Ta fada cewa kididdiga ya nuna Najeriya zata zama kasa mafi girma ta uku a duniya nan da 2045, saboda haka kamata ya yi ta tashi tsaye wajen samarwa yara ilimi.

Wani daga cikin wadanda ‘ya’yansa biyu ke cin gajiyar shirin Mal. Dottiwa Adamu ya fada a hirar mu da shi cewa albarkacin wannan shirin, yanzu haka suna karbar karatun boko.

Ga sauran rahoton daga bakin wakilinmu Sanusi Adamu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

XS
SM
MD
LG