Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’ar Amurka Dake Yola Ta Sake Kaddamar Da Shirin Taimakawa Almajirai


Almajiri
Almajiri

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar karuwar yawan almajirai kan tituna, hakan yasa Jami’ar Amurka da ke Yola a jihar Adamawa, ta sake kaddamar da shirinta na koyar da ciyar da almajirai a karo na biyu.

Da take kaddamar da shirin shugabar jami’ar Farfesa LeGene Quesenberry, ta yabawa malaman dake karantar da yara almajiran, ta kuma ce su kansu yaran abin a yabawa ne saboda kokarin da suke nunawa wajen inganta rayuwarsu a nan gaba.

Shi kuma Mallam Abubakar Abba Tahir, jami’in bangaren yada labarai da sadarwa na jami’ar, ya ce muhimmancin ilimi ne yasa jami’ar bullo da shirin.

Haka nan Abba Tahir, ya ce an tsara shirin ne a bisa tsarin karatun Jeka-ka–dawo.

Imam Aliyu Hassan wani malamin tsangaya ne daga jihar Taraba,ya yaba da wannan tsari da jami’ar Amurkan ta kirkiro to amma yace ya kamata suma ake tunawa dasu.

Inda su kuwa wasu almajiran da jami’ar Amurkan ke taimakawa ke ganin kwalliya na biyan kudin sabulu a yanzu, domin har sun iya karatu da rubutu.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul'aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG