Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar dake jan ragamar mulkin Turkiya ta doshi samun gagarumin nasara


Prime Ministan Turkiya, Tayyip Erdogan da matarsa Emine, suke dagawa magoya bayansu hannu.

A yayinda aka kusan samun dukkan sakamakon zaben wakilan Majalisar wakilan kasar Turkiya, alamu sun nuna cewa jam'iyar Prime Minista Erdogan ta doshi samun gagarumin nasara.

Sakamakon zaben wakilan Majalisar wakilan kasar Turkiya da kusan kamalla samu, sun nuna cewa, Prime Ministan kasar da jam'iyarsa sun doshi samun gagarumin nasara a wannan zabe da aka yi yau lahadi.

Rahotanin da bana hukuma ba, suna fadin cewa jam'iyar Justice and Development ko AKP a takaice, wadda take jan ragamar mulkin Turkiya ta samu kimamin kashi hamsin daga cikin dari. Jam'iyar masu hamaiya ta CHP kuma tana da kimamin kashi ashirin da shidda daga cikin dari, yayinda ita kuma jam'iya ta uku wajen girma a kasar, jam'iyar National Action take da kimamin kashi goma sha uku daga cikin dari.

Duk da gagarumin nasarar da ake sa ran jam'iyar AKP zata samu, da alama ba zata samu rinjayen kashi biyu daga cikin uku da take bukata a Majalisar mai wakilai dari biyar da hamsin, domin ta gabatar da sabon tsarin mulki.

Sakamakon farko sun nuna, saura kiris jam'iyar AKP ta samu kujeru dari uku da talatin da shidda da take bukata, a saboda haka tilas ta nemi goyon bayan wasu jam'iyu.

Duk da cewa, an gudanar da zaben na yau cikin lumana, kamfanin dilancin labarun Anotolia ya bada labarin cewa sai da yan sanda suka kama mutane talatin da hudu a lardin Batman, inda galibin mazauna yankin Kurdawa ne. An kama su ne bisa zargin cewa suna kokarin ganin mutane sun yan takara Kurdawa yan yandipenda

XS
SM
MD
LG