Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar masu ra'ayin rikau a kasar Girka ta kasa kafa gwamnatin gamin gambiza


Zabe a kasar Girka, daya kasa haifar da gwamnatin kawance ya zuwa yanzu

Shugaban jam'iyar masu ra'ayin rikau a kasar Girka, Antonis Samaras yace, ya kasa kafa gwamnatin kawance

Shugaban jam'iyar masu ra'ayin rikau ta kasr Girka, Antonis Samaras, yace ya kasa kafa gwamnatin kawance.

Shugaban kasar Girka, Karolos Papoulias ya baiwa Mr Samaras, wanda jam'iyarsa ta New Democracy ta samu kuri'u mafi yawa a zaben da aka yi a kasar Lahadin nan, damar farko daya kafa gwamnati.

To amma bayan tattauna a yau litinin, Mr Samaras ya kasa shawo kan sauran jam'iyun siyasar kasar, da su hada kai da jam'iyarsa domin su samu rinjaye a Majalisar dokokin kasar mai wakilai dari uku.

A saboda jam'iyar data zo ta biyu ita zata yi kokarin samun goyon bayan jam'iyu domin kafa gwamnatin kawance. Idan itama ta kasa samun nasara, to jam'iyar data zo ta uku ita za'a baiwa wannan dama.

A halin da ake ciki kuma, shugabanin kasashen turai da suka dan tsorata suna ci gaba da matsawa kasar Girka lambar taci gaba da mutunta ka'idodin ranche kudin da aka bata na ceto.

A lokacinda suka jefa kuri'a, alamun sun nuna cewa yan kasar Girka sunfi goyon bayan jam'iyun da basu goyi bayan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da aka cusa wa kasar domin a bata rance fiye da dala biliyan uku na ceto. ba.

XS
SM
MD
LG