Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamiyar PDP ta Sha Kashi a Jihar Osun


APC

Hukumar zabe ta Najeriya ta bayana Rauf Aregbesola, na jamiyar APC a matsayin wanda ya lace zaben Jihar Osun

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, a jihar Osun ta bayana Rauf Aregbesola, na jamiyar APC a matsayin wanda ya lace zaben da aka gudanar a jiya a jihar ta Osun.

Farfesa, Bamitade Omole, na jami’ar, Obafemi Awolowo dake Ile Ife, ne babban jami’an da ya bayana sakamakon zaben da misalin karfe takwas na safiyar yau lahadi.

Farfesan, yace biyo bayan cika kaidodin doka da kuma samun kuriyu mafi yawa, ya kasance wanda yayi nasara a wannan zaben da aka gudanar na Gwamna.

Wanda ya lace zaben Rauf Aregbesola, na jamiyar APC ya samu kuriyu 394,684 a yayin da Iyiola Omisore, na jamiyar PDP ya samu kuriyu 292,747 da bayyana sakamakon sai magoya bayan jamiyar ta APC suka bazama cikin gari da murna.

Kola Ajao, sakataren rikon kwarya na jamiyar PDP a jihar Osun, yace “ ban sa hanu akan takardan sakamakon zaben ba saboda mu ‘yan jamiyar PDP muna da namu kudirin.”

Shi kuwa Imam Bashir, jigo a jamiyar APC kuma mai baiwa gwamnan jihar Osun shawara, a game da harkokin ‘yan arewa, da aiyuka na masamman cewa yayi godiya ga Allah shine abun yi.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG