Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar ANC Dake Mulki A Afrika Ta Kudu Ka Iya Sha Kayi A Zabe


Masu neman wa tattalin arzikin Africa Ta Kudu 'yanci daga kokarin da Shugaba Zuma ya keyi na mamaye arkin kasar
Masu neman wa tattalin arzikin Africa Ta Kudu 'yanci daga kokarin da Shugaba Zuma ya keyi na mamaye arkin kasar

Ta dalilin zarge zargen anfani da dukiyar kasar domin gyara gidansa na kansa lamarin da ya kai har wata kotun kasar ta tilasta masa ya biya gwamnati wasu kudade, jam'yyar shugaba Zuma ka iya sha kayi a zaben kananan hukumomi

Wani mamban babbar jam’iyar Democratic Alliance dake adawa a Afrika ta Kudu, ya ce kalaman da shugaba Jacob Zuma ke yi, tamkar shure-shure mutuwa ne, domin ya san cewa jam’iyarsa ta ANC za ta sha kayi a zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar Laraba mai zuwa.

A ranar Lahadi, Shugaba Zuma ya yi kira ga ‘yan kasar da su zabi jam’iyya mai mulki ta ANC, domin jam’iyyar ta ci gaba da samar masu ababan more rayuwa.

Ita dai jam’iyar ta ANC, ita ke da rinjaye a birane 278 da ke kasar, amma kuria’r jin ra’ayin mutane da aka gudanar, ta nuna cewa akwai yiwuwar jam’iyar ta ANC ta sha kayi a biranen Pretoria da Johannesburg da Port Elizabeth.

ANC, jam'iyyar Zuma dake son a zabeta a zaben kananan hukumomi
ANC, jam'iyyar Zuma dake son a zabeta a zaben kananan hukumomi

Tsohuwar jakadar Afria ta Kudu Sheila Camerer, kuma mamba a jam’iyyar ta Democratic Alliance, ta ce a wannan karo, ‘yan kasar da dama ba za su saurari kalaman Zuma ba, domin sun san cewa babu wani sauyi a rayuwarsu.

Ta kuma zargi shugaba Zuma da yin amfani da dabaru na yaudara domin mutane su zabi jam;iyar ta ANC.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG