Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar APC Mai Hamayya Ta Kauracewa Taron Kasa Menene Dalilinta-Gwamna Wamako


APC
APC

Da yake bayani kan dalilin kauracewa taron Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamako, yace dukkan shugabannin siyasar Najeriya duka da oda ce ta kawo su kan mukamansu, amma yau sai aka wayi gari, jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ko shugaba Goodluck Jonathan, suka maida kasar ta koma tsarin kama kariya.

Gwamna Aliyu Wamako wanda ya tattauna da wakilin Sashen Hausa Umar Farouk Musa, ya kare rashin halartar taron inda aka tabbatarwa Suleiman Abba, zama sabon speto janar na 'Yansandan Najeriya, cewa babu amfanin zuwansu muddin yin hakan zai kara karfafawa kama kariya.

Taron kasa wadda tsoffin shugabannin kasa, da tsoffin manyan alkalan Najeriya da wasu mashahuran masu mulki suke halarta, anan ne ake bitar batutuwa da suka shafi tsaro da kuma tabbatarwa wasu manyan jami'an tsaro mukamansu, kamar yadda aka yiwa sabon speto janar 'Yan sandan Najeriya Suleiman Abba a taron da aka yi ranar Talata.

Wannan mataki da suka dauka, martani ne da jam'iyyar adawar ta fara dauka na bayyana rashin jin dadinta kan wasu matakai da jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriyar tayi, ta bada umarnin janye jami'an tsaro da suke bada kariya ga kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Malam Aminu Waziri Tambuwal.

Ga Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG