Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bata Sake Zani A Zaben 'Yan Majalisar Dokokin Kamaru.


Shugaban Kamaru Paul Biya

Sakamakon zaben majalisar dattawan Kamaru bai haifar da wani abun mamaki ba saboda gwamnati ta lashe kujeru 63 cikin 70.

Jam'iyyar dake mulkin kasar Kamaru ta shugaba Paul Biya, ta lashe kujeru 63 yayinda jam'iyyar adawa ta sami kujeru bakawai.

Majalisar dattawan Kamaru tana da kujeru 100 ne amma 70 ake takara kai, saura kuma shugaban kasa zai nada 'yan majalisa 30 su cika guda darin, kamar dokokin kasar suka tanadar.

Barrister Yahaya na jam'iyyar gwamnati a jihar arewa mai nisa, ya ce ya yi farin ciki da nasarar da suka samu a zaben.

Alhaji Ibrahim Maiyaki a jam'iyyar adawa ya ce dama suna tsammanin hakan ta faru saboda gwamnatin kasar ce ke shirya tsarin zaben yadda ta ga dama. A halin da ake ciki a kasar babu yadda jam'iyyar adawa zata ci zabe. A cewarsa kujeru bakwai din da suka basu, sun yi kokari. Injishi abun da suke jira yanzu shi ne a fito a yi zaben raba kasa su koma gefe daya a rabu da juna.

Amma wani masanin harkokin siyasar Kamaru ya ce a kasar akwai dokoki daban daban na dimokradiya sai dai nan da kwana goma suna jiran Shugaba Paul Biya ya nada 'yan majalisa 30. Yin hakan ne zai bashi damar gudanar da mulkinsa.

Ga rahoton Awal Garba da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG