Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Kwaminis Ta China Ta Bayyana Sabon Tsari da Shugabanninta


Sabbin shugabannin China
Sabbin shugabannin China

Jam'yyar Kwaminis mai mulkin kasa China da fito da wani sabon tsarin shugabanci tare da bayyana shugabanninta amma ba tare da nuna wanda zai gaji shugaban na yanzu ba kamar yadda aka saba gani a kasar

Jam’iyyar ‘yan Kwaminis mai mulki a China, ta bayyana sabon tsarin shugabanninta wadanda zasu rika yanke hukunci a kasar, wacce karfin tattalin arzikinta shine na biyu a duniya..

Sai dai kuma sabanin yadda aka saba a bisa al’ada, a wannan karon ba wata alama dake nuna wanda zai gaji shugaban, hakan yasa masu fashin baki ke ganin wannan wata alama ce dake nuna cewa yanzu shugaban China Xi Jinping na da karfin yin abinda ya ga dama, ba tare da an ja da shi ba.

Zhang Ming, mai fashin baki kan harkokin siyasa, wanda a kwanan nan ne yayi ritaya daga jami’ar Renmin dake birnin Beijing, ya ce shugaba Xi ya sauya tsarin shugabancin kasar, inda ya rage kimar kwamitin gudanarwa na kasar, ya mayar da su ba komai ba.

Firimiya Li Keqiang da Xi Jinping su kadai ne suka rage kan mukamansu a kwamitin, yayin da sauran mambobin biyar suka yi murabus.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG