Da misalin kafe daya na safiyar Lahadi Farfasa Isaac Isuzu jami'in zaben ya bayyana a ofishin hukumar zabe ta INEC dake Ado Ekiti inda ya bayyana sakamakon zaben.
Bayan da aka bayyana Ayo Fayose a matsayin wanda ya ci zaben sai magoya bayan PDP suka fantsama akan tituna suna murna.
'Yan takara goma sha takwas suka fafata a zaben da Ayo Fayose ya lashe. Mr. Banjo Oni yace a gaskiya hukumar zabe tayi adalci kuma tayi aiki mai kyau. Wani da yayi magana yace rawar da Ayo Fayose ya taka a wancan lokacin da yayi gwamna yasa mutane suka fito suka sake zabarsa.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.