Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyu Na Dada Tallata Alamominsu


Buhari da Jonathan.

Yayin da zabukan 2015 ke kara matsowa, jam'iyyu na dada tallata alamominsu da manufofinsu.

Yayinda jam’iyyu ke cigaba da zafafa zawarcin masu kada kuri’a don su yi nasara a zabukan da ke tafe, ana kuma kara jaddada abubuwan da ke bambamta jam’iyyun kamar kaloli da kuma alamomi.

Wakilinmu a Kaduna Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya yi nuni da cewa kowace jam’iyya na da alamomi kuma na jaddada alamomin don bambamta ta da sauran jam’iyyun. Y ace ABGA na amfani da alamar zakara DPN na amfani da alamar tocila APC na amfani da tsintsiya sannan kuma PDP na amfani da laima.

Wakilin namu ya lura cewa ‘yan APC na matukar amfani da tsintsiya a yayin da kuma PDP ke amfani da laima. Saboda haka wakilin namu ya shiga kasuwa don binciken cinikin laima da tsintsiya.

Ya ruwaito ‘yan kasuwa na cewa an fi cinikin tsintsiya saboda yawan amfani da ita a harkokin yau da kullum. Wani dan kasuwa mai suna Dan Jalele da ke kan kwana mai shago ya ce, “Gaskiya tsintsiya alhamdulillahi ko da yaushe mu na cin gajiyarta. Ka ganta nan, idan na sayo ta kai dari biyu ba ta wuce kwana biyar an kwashe ta. Ba za a taba hada tsintsiya da laima ba. Mutuncinsu da martabarsu ba daya ba ne saboda ita tsintsiya kullum da amfaninta. Haka wani mai suna Dari CID shi ma ya fada.

Shi ma wani mai suna Amin mai Laima ya ce rabon ya yi cinikin laima ya kai watanni uku. Ya ce lokacin ruwa ne kawai aka fai cinikin laima.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG