Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Zata Hada Hannu Da Najeriya A Fannin Kiwon Lafiya


Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yiwa Mahajjata gwajin cutar Ebola.
Jami’an kula da lafiyar matafiya na duba fasfo kafin su yi amfani da ma’aunin zafin jiki su yiwa Mahajjata gwajin cutar Ebola.

Gwamnatin kasar Jamus, da kuma jihohin Oyo da Kano a Najeriya, sun fara wani shiri da zai sanya ido a game da barkewar cututuka, tare da daukar matakin gaggawa na shawo kansu.

Wannan shirin dai zai fara aiki ne a jihohin Oyo da Kano a matsayin matakin farko da zai wanzu zuwa wadansu jihohin Najeriya a nan gaba ba da dadewa ba.

Daya daga cikin wakilan kasar Jamus, Profesa Jerid Kurias da ya jagoranci tawagar kasar Jamus zuwa jihar Oyo domin fara shirin ya bayyana cewa, sun je jihar Oyo ne domin neman hanyar fara aiwatar da shirin ba tare da bata lokaci ba, da kuma gudanar da bincike da nufin ganin shirin ya yi nasara.

Wani Malami na amfani da na’urar auna zafin jiki domin neman alamun cutar Ebola.
Wani Malami na amfani da na’urar auna zafin jiki domin neman alamun cutar Ebola.

A nata bayanin daya daga cikin wakilan gwamnatin Jamus, Dr Gabriela ta bayyana cewa, sa ido zai taimaka wajen shawo kan barkewar cututukan da kuma maganinsu.

Cututukan da za a sawa ido sun hada da kwalara, cutar Ebola, murar tsuntsaye da dai sauransu. Za a gudanar da aikin ne ta wajen amfani da wayar salula ta zamani.

Ga rahoton da wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal ya iko mana.

Rahoton Kiwon Lafiya a Najeriya -1' 57"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG