Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Janar Buhari Yace Bashi Da Wani Shakku Game Da Zabe Mai Zuwa


Janal Muhammadu Buhari.

‘Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar hamaiya ta APC Janaral Muhammdu Buhari, yace bashi da wani shakku gameda yin zabe a Nigeria.

‘Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar hamaiya ta APC Janaral Muhammdu Buhari, yace bashi da wani shakku gameda yin zabe a Nigeria.

Janaral Buhari yayi wannan furuci ne daga London a hirar da Aliyu Mustapha Sokoto yayi dashi.

Yace idan dai ba canjin mulki zasu yi ba, in dai za'a bi ka'idodin kundin tsarin mulkin Nigeria, ba makawa dole su yi wannan zabe. Yace makon shiddan da aka kara, hukumar zabe ta kure malejinta, idan suka daga sun yi canjin mulki, wannan kuma tsakanin su da sauran 'yan Nigeria, inji Buhari.

Haka kuma Janaral Buhari yayi magana akan ikirarin da shugaba Jonathan na Nigeria yayi cewa, za'a kama Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram. Yace ai jam'iyarsa ta bada amsa

akan wannan ikirari. A baya gwamnatin Nigeria tace an kashe Shekau, yaya kuma za'a yi suke Shekau yana da rai yanzu.

Akan zargin da gwamnatin Nigeria tayi cewa Buhari ne ke daurewa Shekau gindi, idan ta kama shi zai fadi haka. Buhari yace yana jiransu.

XS
SM
MD
LG