Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Buhari Ya Aza Laifin Tarzomar Bayan Zabe Kan Bata Gari


Tarzoma ta barke a Kano bayan zaben shugaban kasa
Tarzoma ta barke a Kano bayan zaben shugaban kasa

Jam’iyyar CPC tana kira ga magoya bayanta kada su yar da da abinda ta kira wasu bata gari suna fakewa dasu suna barnar rayuka da dukiyoyin jama’a,da sunan bayyana rashin amincewar su da sakamakon zaben shugaban kasa

Saurari Jawabin Janar Buhari a kasa

Hirar Janar Buhari

Jam’iyyar CPC tana kira ga magoya bayanta kada su yar da da abinda ta kira wasu bata gari suna fakewa dasu suna barnar rayuka da dukiyoyin jama’a,da sunan bayyana rashin amincewar su da sakamakon zaben shugaban kasa da aka bayyana.

Dan takarar shugaban kasa,kuma tsohon shugaban kasa a zamanin mulkin soja Janar Muhammadu Buhari ne, ya yi wan nan kira lokacin da yake magana da manema labarai kan tarozmar da ta biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban Najeriya.

Janar Buhari yace “ ta’asar kona wuraren ibadu da wasu laifuffuka da aka aikata” sun dara ma satar kuri’a da aka yi.

Dan takarar shugaban kasan ya bayyana godiya magoya bayan jam’iyyar, ya kuma nemi su kara hakuri,jam’iyyar zata dauki matakan kwato musu hakkinsu.

XS
SM
MD
LG