Accessibility links

Janaral Buhari Yayi Gangamin Neman Zabe a Yola Jihar Adamawa


Janaral Muhammad Buhari

Yayin da yake jawabi a wurin gangamin Janaral Buhari, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karfafa magoya bayansu su fito su zabi APC

A jawabinsa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Janaral Muhammad Buhari ya tabo wasu matsalolin dake addabar Najeriya inda yace idan aka zabesu zasu yi maganinsu.

Yace cikin shekaru goma sha shida da PDP tayi mulkin kasar ta kashe jama'ar kasar ta kuma kashe kasar. Saidai Allah yayi taimako a farfado da ita. Yace sun fishi sani halin tabarbarewar tsaro a jihar domin har yanzu kananan hukumomi biyu suna hannun 'yan ta'ada.

Aikin farko da zasu fuskanta shi ne a kyautata tsaro domin al'umma su samu walwalar zuwa duk inda suke so su je dare da rana ba tare da jin tsoro ba. Zasu karfafa sha'anin noma domin mutane su samu aikin yi.

Ambasada Fati Balla ita tayi jawabi a madadin matan jihar Adamawa. Tace sun san mata da yawa sun bar gidajensu sabili da dalilan tsaro. Idan Alllah ya kawo Janaral Buhari duk zasu koma gidajensu.

Mutane da yawa suka yi tattaki daga wurare daban daban domin su kasance wurin gangamin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

XS
SM
MD
LG