Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaruma Fati K.K. Ta Yi Aure


Jaruma Fati K.K. (Hoto: Shafinta na Instagram)

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood a arewacin Najeriya, Fati K.K. ta yi amarce.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a ranar Juma’a, ko da yake ba ta ambaci ranar da aka daura auren ba.

“Allah ka ba mu zaman lafiya ni da mijjina. Ya Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu.” Jarumar ta wallafa a shafin na ta na Instagram.

Abokanan sana’arta da masoyanta sun mamaye shafinta da sambarka da taya ta murna.

“Fatima wannan abin da na gani nake kuma ji ana yi miki murna da gaske ne aurenki aka daura? Wani mai bibiyan shafinta, mai suna nurafatikk, ya tambayi jarumar a shafinta.

Fati K. K. (Hoto: Shafin Instagram din ta)
Fati K. K. (Hoto: Shafin Instagram din ta)

Kuma nan da nan ta ba shi amsa “Eh,” ta ce.

Kadan daga cikin fina-finan da suka fito da Fati K.K. a masana’antar ta Kannywood, sun hada da “Mijina ne,” inda ta fito da jarumi Ali Nuhu da kuma Shu’aibu Lawal wato Kumurci.

Sai kuma fim din “Carbin Kwai,” ita da Ali Nuhu da kuma “Miyetti Allah,” wanda suka yi tare da Ibrahim Maishunku.

Jarumai irinsu Halima Atete, Aisha Tsamiya, General BMB da Baballe Hayatu na daga cikin wadanda suka taya ta murnar.

Dubi ra’ayoyi

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG