Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumin "The Wire" Michael K. Williams Ya Rasu


Marigayi Michael K Williams a shekarar 2018
Marigayi Michael K Williams a shekarar 2018

Williams ya fara shiga fannin nishadi ne a matsayin dan rawa inda ya fito a wakokin Missy Elliot, Ginuwine, Crystal Waters da kuma Technotronic.

Fitaccen jarumin Hollywood Michael K. Williams wanda ya taka rawar Omar Little a fim din “The Wire” ya rasu. Shekarunsa 54.

An tsinci Williams ne a mace a gidansa da ke yankin Brooklyn a New York a ranar Litinin.

‘Yan sandan birnin New York na binciken mutuwar jarumin akan yiwuwar ya sha kwayar da ta wuce kima a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Williams, ya kasance jarumin da ya fi fice a fim din na “The Wire” wanda kamfanin HBO ya watsa daga 2002 zuwa 2008.

Baya ga fim din na “The Wire” Williams ya fito a wasu manyan fina-finai irinsu “Boardwalk Empire” wanda shi ma kamfanin HBO ya watsa a tsakanin 2010 zuwa 2014, sai “Twelve Years a Slave,” da kuma “Assasin’s Creed.”

Michael K Williams
Michael K Williams

Amma rawar da ya taka a matsayin Omar, ita ta hasakaka tauraronsa, kamar yadda ya taba fada a hirar da aka yi da shi a shirin Stephen Colbert “The Late Show’” a 2016.

An haifi Williams a shekarar 1966 a Brooklyn, mahaifiyarsa daga yankin Nassau take a Bahamas, mahaifinsa kuma mutumin kudancin California ne. Ya yi karatunsa a makarantar George Westinghouse.

A karon farko da ya shiga harkar nishadantarwa, Williams ya fara fitowa ne a matsayin dan rawa a wakokin Missy Elliot, Ginuwine, Crystal Waters da kuma Technotronic.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG