Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaba Obama Da Mataimakinsa A Babban Taron Democrat


Shugaba Obama a babban taron jam'iyyar Democrat
Shugaba Obama a babban taron jam'iyyar Democrat

Shugaban Amurka Barack Obama da Mataimakinsa Joe Biden, sun yi jawabi a rana ta uku a babban taron Democrat da ake yi a Philadelphia, inda Biden ya jinjina ma na gaba da shi, Shugaba Barack Obama, ya kuma jaddada cancantar 'yar takarar jam'iyyarsu a zaben shugaban kasar na 2016, Hillary Clinton.

Biden ya gaya ma wakilan zabe na delegates da daren jiya Laraba, cewa babu mai kaunar Amurka kamar Hillary Clinton. Amurka wani bangare ne na rayuwarta, a cewarsa.

Shugaba Obama, wanda ya yi babban jawabi da daren, wanda ya kuma gaya ma Amurkawa dalilansa na ganin cewa Hillary Clinton, wadda ta taba zama Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka a karkashin gwamnatinsa, ya kamata ta gaje shi a Fadar ta White House bayan da ya bar ofis a watan Janairu mai zuwa.

A wani dan bangaren jawabin na Shugaba Obama, wanda aka yada 'yan sa'o'i kafin jawabin nasa, Shugaba Obama ya ce ba a taba samun wani tumum, na-miji ko ta-mace ba, da ya fi Hillary Clinton cancantar zama Shugaban kasar Amurka.

"Babu abin da zai taimaka maka wajen shiryawa ta hakika, don tinkarar kalubalen matsayin Shugaban kasa. Kafin ka zauna kan kujerar, ba za ka san abin da ake nufi da yin tozali da matsalolin kasa da kasa ba, ko kuma batun tura matasa zuwa fagen daga. To amma Hillary Clinton ta taba aiki a ofis din, ta sha taka rawa a shawarwarin da ake yankewa.

Haka kuma ta san abin da ya dace wurin shawarwarin da gwamnatocinmu ke yankewa don amfanar ma'akata, da dattawa da masu kananan kamfanoni, da sojoji da tsoffin sojoji. Kuma har a tsakiyar matsala, ta kan iya sauraron mutane, ta kuma natsu; ta girmama kowa da kowa. Kuma duk yadda matsala ta ke, duk yadda aka so galabaitar da ita, sam ba ta mika kai."

XS
SM
MD
LG