Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Jebun Magunguna Milyan 82 A Afirka.


Jami’an kastam sun ce sun kama jebun magunguna da wadanda suka sabawa ka’ida milyan 82, a somame da suka kai a kasashen Afirka 16.
Kungiyar jami’an kastam ta duniya, ta ce an kama wadannan magungunan ne cikin watan Yuli, lokacinda suka kai farmakin a tashoshin ruwa na kasashe a gabashi da yammacin Afirka.
Wani mutum a kasar Cambodia yake sayen maganin zazzabin chzon sauro.
Wani mutum a kasar Cambodia yake sayen maganin zazzabin chzon sauro.

A cikin sanarwa da kungiyar ta bayar jiya Alhamis, kungiyar tace ta kama jebun magunguna mafiya yawa a Angola, Togo, Kamaru, da kuma Ghana.
A hira da Muriyar Amurka, babban sakataren kungiyar jami’an kastam, Kunio Mikuriya, yace galibin magunguna da aka kama suna iya zama hadari gag a jama’a.

Mr. Mikuriya yace galibin jebun magungunan da aka kama, sun fito daga kudanci da gabashin Asiya, da kuma Gabas ta tsakiya. Yace jami’an da suka gudanar da binciken sun shaidawa hukumomin kasashen da lamarin ya shafa sabo da su kama wadanda suke da hanu wajen shigo da mgungunan.
Sauran kasashenda aka gudanar da somamen sun hada da Benin, jamhuriyar demokuradiyyar Kwango, Ivory Coast, Gabon, Guinea,Kenya, Laberiya, da Muzambique, Najeriya, Senegal da Tanzania.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG