Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jebun Magungunan Malaria Suna Barazana Ga Yaki Da Cutar


Ana taimakawa wata mace a Sudan ta makala gidan sauro.
Ana taimakawa wata mace a Sudan ta makala gidan sauro.

Wani sabon bincike ya nuna cewa jebun magungunan zazzabin cizon sauro da aka cika kasuwannin Afirka da Asiya a fiyeda shekara 10 da suka wuce suna mummunar barazana kan kokarin yaki da wan nan cuta.

Wani sabon bincike ya nuna cewa jebun magungunan zazzabin cizon sauro da aka cika kasuwannin Afirka da Asiya a fiyeda shekara 10 da suka wuce suna mummunar barazana kan kokarin yaki da wan nan cuta.

Rahotun da cibiyar hukumomin kiwon laifya ta Amurka wallafa ya nuna bayanai da aka tattara daga kasashen dake kudu da Hamadan sahara 21, binciken ya nuna kashi 35 cikin magungunan yaki da Malaria ba a hada su da kyau ba, yayinda kashi 20 na magungunan jebu ne.

Wasu alkaluman kan nazari da aka yi wa magungunan yaki da cutar daga kasashe 7 a yankin Asiya, sun nuna kashi 35 cikin dari na magungunan sun gaza a gwaji da aka yi, kusan rabi ba a hada su dai dai ba, san nan kashi 36 cikin dari kuma baki daya jebu ne.

Masu bincike sun ce sai tayu lamarin yafi haka muni, domin wasu matsalolin ba a bada rahoto akansu ba, kuma wasu mutane suna jinyar kansu ta sayen magani ba tareda sanin likita ba.

Fiyeda mutane bilyan uku a fadin duniya suke da kasadar kamuwa da cutar malaria, cutar tana kashe kusan mutane milyan daya a ko wace shekara, galibinsu jarirai da yara daga nahiyar Afirka.

Masana kimiyya suka ce amfani da jebun magunguna ko magunguna da basu da tasiri sosai suna iya taimakawa cutar ta gawurta kamar yadda aka fara gani akan iyakokin kasashen Tahiland da Cambodia.

XS
SM
MD
LG