Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Niger Ta Karfafa Matakan Tsaron A Lokacin Bukukuwan Sallar Layya


Alhaji Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Niger
Alhaji Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Niger

Saboda tabbatar da zaman lafiya a lokacin bikin sallah mai zuwa, gwamnan jihar Niger ya gana da duka shugabannin jami'an tsaro da duk sarakunan gargajiya domin cimma matsaya akan tsaro a jihar

Biyo bayan ganawar da Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi da jami'an tsaro da sarakuna, rundunar 'yan sandan jihar ta ce za ta girke 'yan sanda 2,030 a wurare daban cikin jihar, domin tabbatar da an gudanar da bukuwan sallah lami lafiya.

DSP Abubakar Dan Inna, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar,ya ce zasu maida hankali ne a wuraren da suke ganin akwai bata gari a cikin bayanin da ya yiwa Sashen Hausa.

Shi ma kakakin gwamnan jihar Jibril Baba Ndagi, ya tabbatar da zaman shawarwari da gwamnan da jami'an tsaro da kuma sarakunan gargajiya dake jihar suka yi.

Sai dai al'ummar yankin Sarkin Pawa, da Shiroro masu iyaka da jihar Kaduna, suna ci gaba da fargaba akan janye jami'an tsaro da aka yi a yankin nasu duk da cewa suna fama da masu garkuwa da mutane suna karban kudin fansa.

Alhaji Adamu Erana, wani dan siyasa a yankin yayi kiran da adawo da jami'an tsaron da aka kwashe daga yankin. A cewarsa masu garkuwa da mutane suna ci gaba da satar mutane kuma sai an ba da kudi su sako su.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG