Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar California Na Barazanar Barin Tarayyar Amurka Domin Trump


Dalibai a jihar California suna zanga zanga a gaban majalisar jihar basa son Trump

A wani gefen kuma...wasu mutanen babbar jihar nan ta California, wadanda suka jefa wa Hillary Clinton kuri’u masu yawan gaske, sun fara barazanar fitar da jihar tasu daga cikin Amurka don su nuna cewa basa kaunar Donald Trump ya zamar musu shugaban kasa.

Dangane da hakan ne akace wasunsu sun fara koyi da abinda ya faru a Biritaniya bayan kuri’aar da aka jefa kan ci gaban zamanta a cikin Kungiyar kasashen Turai (abinda aka radawa suna “Brexit”), shine suma mutanen na jihar ta California masu ra’ayin ballewa, suka fara barazanar cewa California za ta fice daga Amurka don nuna adawar tasu ga Trump.

A California masu zanga-zangar suna godewa Obama amma basa son Trump
A California masu zanga-zangar suna godewa Obama amma basa son Trump

Jihar California dai itace jihar da tafi duk jihohin Amurka yawan mutane don kashi 16 cikin100 na daukacin dukkan mutanen Amurka din suna cikin wannan jihar ne.

Haka kuma in abin California ta balle ne daga Amurka, zata zama kasa ta 35 a girma a duk duniya, ga ta kuma itace ta shidda a yawan arziki a duniya, a cewar wasu alkalumman kiddiga da aka bada a shekarar da ta gabata ta 2015.

XS
SM
MD
LG