Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Hawaii Ta Kalubalanci Sabuwar Dokar Shugaba Donald Trump


Dough Chin
Dough Chin

Jihar Hawaii ta zama jiha ta farko da ta shigar da kara domin kalubalantar sabon umarnin da shugaban kasa Donald Trump ya zartar na hana kasashe shida da galibi Musulmi ne shiga Amurka.

Lauyoyin jihar sun shigar da karar ne jiya Laraba da yamma a kotun gwamnatin tarayya dake Honolulu, inda suka bayyana cewa, dokar zata yi barazana ga al’ummar Musulmi da ‘yan yawon bude ido da kuma daliban kasashen ketare.

Lauyan lardin Hawaii Dough Chin ya bayyana cewa, umarnin nuna wariya ce a kan mutane bisa ga kasar da suka fito, ko addininsu.

Majalisa ta tsaida shawara a shekara ta dubu da dari tara da sittin da biyar cewa, ba za a ci gaba da nunwa jama’a wariya sabili da kasarsu ta asali ba. Kuma wannan yana cikin dokar shige da fice. Saboda haka, matsalar wannan umarnin shugaban kasar ita ce, ta maida mu baya kafin shekara ta dubu da dari tara da sittin da biyar.

Wani alkalin kotun gwamnatin tarayya zai saurari karar ranar goma sha biyar ga watan Maris, kwana daya kafin umarnin ya fara aiki.

An cire kasar Iraq a sabuwar dokar da ta hada da kasashe shida dake cikin jerin kasashen da shugaba Trump ya sa a umarnin na farko.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG