Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Jigawa Ta Soma Yaki Kan Cutar Tarin Fuka da Kuturta


Wata mai cutar kuturta

Kwamitin lafiya, sadaswa da wayas da kan jama’a wanda ke karkashin sashen yaki da cutar tarin fuka da kuturta ta jihar Jigawa, ta yi ziyarar wayar da kan jama’a a masarautu biyar a jihar.

Kwamitin lafiya, sadaswa da wayas da kan jama’a wanda ke karkashin sashen yaki da cutar tarin fuka da kuturta ta jihar Jigawa, ya yi ziyarar wayar da kan jama’a a masarautu biyar a jihar.

A fadar sarkin Hadeja Alhaji Abubakar Maje, shugaban wannan kwamiti Alhaji Usman Maje Mohammed yace manufar wannan ziyarar shine domin wayar da kan sarakurana game da illar da tarin fuka da kuma kuturta suke da shi da kuma neman hadin kan sarakuna domin yaki da wadannan cututtukan.

Ya nuna cewa Nijeriya ita ce ta10 cikin kasashen da suka fi yawan masu dauke da cutar tarin fuka a Afrika.

Yayinda yake maida martani, sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje yayi murna da kafa wannan kwamiti, kuma yayi alkawarin fadakar da jama’arsa kan wadannan cututtukan. Ya roki kafofin yada labarai da su hada hannu da wannan kwamiti wajen wannan yakin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG