Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Kaduna Ta Haramta Bara da Talla da Sana'ar Achaba


Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wata sanarwa tana bayyana dalilan da suka sa majalisar tsaro ta jihar da ayyana dokar haramta barace-barace da tallace tallace da sana'ar achaba

Inji mai magana da yawun gwamnatin jihar an yi dokar ne da nufin magance duk wata barazana ta tsaro a jihar.

Yayinda yake karin haske akan haramta wadannan sana'o'i ukku a jihar Mr. Samuel Aruwan yace hana tallace tallace ya hada da duk nao'in talla daga yara har zuwa manya. Yace dokar ba sabuwa ba ce amma abu sabo shi ne matsayin gwamnati cewa daga yanzu dokar zata yi aiki ba sani ba sabo.

Duk wanda ya yiwa dokar karan tsaye zai kuka da kansa saboda hukumcin da za'a yi masa.

Tuni mai magana da kungiyar makafin jihar Muktar Saleleko yana cewa ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa. Yace Malam Nasiru Rufai bai basu abinci ba bai kuma basu aikin yi ba saboda haka kamar yadda yace shi baya jin tsoro haka ma nakasassun jihar sun rantse ba zasu bar bara ba a jihar Kaduna saidai idan za'a hallakasu.

Mr. Samuel Aruwan ya bayyana irin tanadin da gwamnatin ta yiwa wadannan mutanen da aka nahasu sana'arsu. Na farko shi ne kare rayukansu. Na biyu za'a inganta masu ilimi da kiwon lafiya. Yace matakin gwamnati an yi ne saboda dalilai na tsaro.

Matasa dake talla a gefen tituna sun maida martani. Sun ce gwamnati ta samar masu abun yi ba ta hanasu ayyukansu na cin abinci ba. Wani ma cewa yayi bai san abun da zai yi ba domin da sana'ar yake taimakawa iyayensa.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG