Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Niger Za Ta Dauki Karin Ma'aikatan Lafiya


Wasu Ma'aikana Kiwon Lafiya a Najeriya
Wasu Ma'aikana Kiwon Lafiya a Najeriya

Karancin ma’aikatan kiwon lafiya na ci gaba da janyo cikas wajen gudanar da ayyukan kula da lafiyar marasa lafiya a Jihar Niger da ke arewacin Najeriya.

Hakan ne ya sa gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello, ya ba da umurnin a dauki karin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan wata ziyarar ba za ta da gwamnan ya kai ne a asibiti inda ya tarar babu likitocin da za su saurari dumbin marasa lafiya da suka yi dafifi.

“Na je asibiti misalin karfe uku har zuwa karfe goman dare babu likita ba, a lokacin na kira sakataren na dindindin a ma’aikatar kiwon lafiya na gaya mai cewa a dauki likitoci a aiki.” In ji Gwamna Bello.

Sai dai masu sa ido kan al’amuran yau da kullum sun ce duk da cewa gwamnan ya yi abin a yaba da ya ba da wannan umurni, kamata ya yi a ce an gudanar da bincike domin a gane wadanne ma’aikatan kiwon lafiya ne ba su je aiki ba a daren.

Baya ga batun matsalar da ke tattare a fannin kiwon lafiyar kasar, akwai rashin abun hanu da ‘yan jihar ke korafin babu, wanda hakan ke sa mutane da dama su fi dogaro a kan asibitocin gwamnati da suka fi sauki

Saurari wannan rahoton Mustapha Nasiru Batsari domin jin yadda al’umar jihar ke kokawa da rashin kudi a hanu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG