Accessibility links

​An fara gudanar da zaben raba gardama a Ukraine.

Yau lahadi, al’ummar jihohi biyu dake gabashin Ukraine ke kada kuri’a kan dacewar ballewa domin kafa tasu kasar.Kuri’ar da al’ummar yankin keyi yau ta nuna irin yadda rikicin siyasa ke neman wargaza hadin kan kasar Ukraine da rabon da ganin haka tun yakin duniya na biyu.

Shugaban rikon kasar Ukraine Oleksandr Turchynov yayi gargadin cewa duk wani matakin da za’a dauka cikin fushi da gagawa na neman ‘yancin kai ba tare da bin ka’ida ba, da wuya ya kai ga cimma nasara, don haka yake yin kira ga ‘yan tawayen da su koma ga teburin tattaunawa domin baiwa yankin cikakken ‘yancin cin gashin kansu.
XS
SM
MD
LG