Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohin Amurka Shida Sun Kalubalanci Sabuwar Dokar Trump


Shugaban Amurka Donald Trump

Jihohi shida a Amurka suna kalunbalantar umurnin Shugaban Kasa Donald Trump da aka sakewa gyarawa da ya hana 'yan kasashe shida da Musulmi suka rinjaye shiga Amurka.

Jihar Hawaii ta gabatar da kara inda take kalubalantar sabon umurnin na gwamnatin tarayya wacce ta ce za ta cutar da Musulmai da suke zaune a jihar dake tsibirin tekun pacific.

Sauran Jihohi biyar sun hada kansu domin kalubalantar sabuwar dokar ta Trump , wacce ake son ta maye gurbin ta farko da kotunan Amurka suka yi fatali da ita.

Babban Attorney Janar a Jihar Washington Bob Ferguson ya ce Jihar ta na da kwakwakwarar madafa akan shari’ar, babu shakka an takaita umarnin a sabuwar dokar ta Shugaban, amma hakan bayana nufin an wanke matsalolin da dokar ta gudanar ba a kundin tsarin mulki.

Jihohin Oregon da Minnesota da New York sun hada kai a matakin shari’ar da Jihar Washington, sai kuma jihar Massachusetts ta bayyana a jiya Alhamis ita ma za ta shiga cikin jerin jihohin a mako na gaba kan kin amincewa da dokar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG