Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jinkiri Da Aka Samu Na Fitar Da Sakamakon Zabe a Iowa Ya Haifar Da Rudani


Tsaikon da aka samu da ba saban ba na fitar da sakamakon zaben fidda ‘yan takara a jihar Iowa na jam’iyyar Democrats ya haifar da ra’ayoyi mabambanta.

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar dai sun isa jihar New Hampshire, domin mataki na gaba na zaben, sai dai basu san matsayin su a zaben na Iowa ba, suna bayyana ra’ayoyin su akan matsalar da aka samu.

Ya yin da wasu suka saka alamar tambaya akan jinkirin, wasu kuma suna tausayawa dalilan da suka haifar da jinkirin.

A bangaren masu zaben ma, an sami ra’ayoyi mabambanta. Paul McClay, ya bayyana damuwa da tsaikon, ya ce “Ina fatar za’a taimaka a zabi dan takara da zai yi wa kasar nan aiki, da kuma sauya ‘yan jam’iyyar Republican da masu zaman kan su da ba’a gamsu da rikon ludayin su ba”.

To sai dai wata mai zabe a Iowa Darryl Eihorn, tana da ra’ayi daban, inda tace, “a’a ba na zargin komai. Ba na tsammanin akwai wanda zai saka ayar tambaya akan sahihancin zaben, idan aka yi la’akari da namijin kokarin da suke yi na tabbatar da adalci da kuma bada sakamako na gaskiya. Don haka ba matsala, za mu jira sakamakon”.

A dai dai lokacin da aka soma bayyana sakamakon zaben da yammacin Talata, hankali kuma ya karkata a jihar Hampshire, inda za’a gudanar da zabe na gaba.

Don cikakken rahoto a saurari Murtala Sanyinna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:33 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG