Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jinkirin Jigilar Maniyattan Adamawa Ya Jawo Gunaguni da Korafi


 Wani ginin makarantar firamari ne wurin kwanan maniyattan jihar Adamawa da suke jiran takardar biza zuwa Saudiya
Wani ginin makarantar firamari ne wurin kwanan maniyattan jihar Adamawa da suke jiran takardar biza zuwa Saudiya

Amiril hajj na jihar Adamawa kuma kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Kabiru Mijinyawa ya ce ba zai yi sassauci ba wajen ladabtar da duk maniyyaci da ya nemi keta sharudda da dokokin hukumar kula da jin dadin mahajjata ko na kasar Saudiyya.

Kalaman Amiril Hajj na jihar Adamawa na zuwa ne biyo bayan gunaguni da koken maniyyatan kan jinkiri da ake samu wajen jigilarsu wanda sau biyu ake soke tashin jirgin lamarin da ya jefa su cikin mawuyacin halin na rashin wajen kwana mai inganci. Suna kwana cikin sauro da ruwan sama a sansanin wucin gadi da ke wata makarantar firamare dalili da ya sa suka nemi yin zanga zanga na nuna rashin jin dadinsu.

Wasu da Muryar Amurka ta yi hira da su Hamza Adamu, Musa Hamza da kuma A'isha Umar wadanda suka share sama da kwanaki biyar a sansanin suna jiran isowar biza sun nuna takaici kan mummunan yanayin da suke zaman jira a ciki tare da kiran a gaugauta samar masu da takardun shiga kasar Saudiyya.

Lokacin da gwamnan jihar Muhammad Umaru Jibirilla ya ziyarci sansanin, hakuri ya baiwa maniyyatan tare da tabbaccin za a gaugauta samar masu da bizar su cikin kankanin lokacin don su sami sukunin sauke farali.

Sai dai hakar wakilinmu Sanusi Adamu ba ta cimma ruwa ba da ya ziyarci ofishin Babban sakataren hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Adamawa Injiniya Abubakar Bobboi don neman bayanin matakan da hukumar ke dauka na kyautata sansanin da kuma na samar masu biza cikin lokaci.

Kawo yanzu jirgin Flynas na kasar Saudiyya ya yi kafa biyu na maniyyatan 839 daga cikin 2600 na wadanda suka cika sharuddan sauke faralinsu bana.

Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG