Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Rasha da Siriya Sun Sake Kai Hare-hare Kan Aleppo


Hare-haren jiragen Rasha da Siriya a Aleppo

Jiragen yakin saman Rasha da na dakarun Syria sun gudanar da wadansu hare-haren sama a yankunan da ‘yan tawaye ke rike da su a birnin Aleppo a cikin daren jiya zuwa wayewar garin yau Juma’a, a cewar wata kungiya mai sa ido akan rikicin.

Kungiyar Syrian Observatory for Human rights ta ruwaito a yau juma’a cewa an kaddamar da hare-haren sama da dama a gabashin Aleppo, kuma bayan an kammala kai hare-haren zuwa tsakiyar safiya, an ci gaba da wasu daidaikun hare-hare a arewaci da kudancin birnin na Aleppo.

Wasu majiyoyi na ‘yan fafatuka, sun ce hare-haren sun kashe ko kuma sun raunata mutane da dama, koda ya ke babu takamaiman adadin mutanen da suka jikkata, domin har yanzu akwai wadanda su ke karkashin baragizan gine-gine.

Wadannan sabbin hare-hare, na zuwa ne kwana guda bayan da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ke shirin ganawa da takwaran aikinsa na Rasha Sergie Lavrov.

Kuma wannan ganawa ita za ta kasance ta farko, tun bayan da Hukumomin Washington da Moscow su ka yanke tattaunawar diplomasiyya a farkon watan nan.

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG