Jirgin dake kan hanyarsa na kwashe mutanen suke fuskantar hadarin tumbudin wuta daga wani tsauni. Duka wadanda suke cikin jirgin sun halaka.
Jiya Lahadi ne jirgin ya afkawa wani tsauni a gundumar da ake kira Temanggung a tsakiyar lardin Java. Hukumar aikin ceto da agaji ta kasar tace an gano gawarwakin duka wadanda suke cikin jirgin.
An shirya sojojin ruwan da kuma masu aikin ceton, zasu taimaka a aikin kwashe mutane a wani tsauni a ake kira Dieng, bayan da wani tsauni ya fara tumbudi har mutane biyar suka jikkata, yayinda ta fara turo laka da toka wadanda tsawon su ya kai mita 50.
Tsaunin Dieng yana da farin jini ga masu yawon bude ido, musamman saboda wuraren ibadar Hindu wadanda aka gina a karni na tara.
Facebook Forum