Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Nan Mai Aiki Da Karfin Rana Ya Isa Jihar California.


Wannan shine jirgin mai aiki da karfin rana.

Jirgin yayi nasarar kammala tafiyarsa mafi hadari na sa'o'i 56, ta kan tekun Pacific

Wani jirgin sama mai aiki da karfin rana, wanda yake kokarin zagaye duniya, ya isa jihar California, bayan da ya kammala zangonsa mafi hadari, bayan da yayi tafiyar sa'o'i 56 ta kan tekun Pacific. Wannan zagon yana da hadari saboda babu wurin sauka na gaggawa, idan bukatar haka ta taso.

Jirgin mai suna Solar Impulse 2, da turanci, ya wuce a sararin dogon gadan nan dake birnin San Farncisco, da ake kira Golden Gate a jiya Asabar, lamari da ya kayatar da msu kallo da yawa.

Jirgin zai ci gaba da shawagi a sararin samaniya har zuwa 12 na daren Asabar agogon yankin, lokacin juyawar iska ta lafa, sannan ya sauka a karamin filin jirgin sama da ake kira Moffett dake yankin kwazazzabun Silicon.

Matukin jirgin Bernard Piccard, yace saukar da jirgin zaiyi a kwazazzabun Silicon, zai taimaka wajen alakanta shirin zagaye duniyar da jirgin ke yi , da irin kwazon yankin, a fannin kere-kere da wasu ci gaban kimiyya da fasaha.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG