Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Ya Kama Da Wuta A Nepal


'Yan agaji a inda hadarin ya auku

A wani al'amari mai ban takaici, mutane akalla 40 sun mutu bayan da jirgin saman da ke dauke da su ya kama da wuta yayin sauka a Nepal.

Jami'ai a Nepal sunce wani jirgin-fasinja wana yake dauke da pasinjoji daga Bangladesh ya fadi ya kuma kama da wuta a lokacin da yake sauka a filin jirgin saman Kathmandu, har yai sanadiyyar kashe a kalla mutane 40.

Shaidun gani da ido sunce jirgin yayi ta tanga-tangal a yau Litinin kafin yayi kokarin sauka a karo na biyu, a lokacin ne ya kama da wutar.

Mai magana da yawun kamfanin jirgin US- Bangla wanda yake da cibiya a Dhaka, yace mutane 71 ne a cikin jirgin har da ma'aikatan sa 4. A cikin pasinjojin 67 kuma 32 'yan asalin kasar Bangladesh ne , 33 'yan Nepal guda kuma dan china da kuma guda dan Maldives.

Jirgin saman mai farfela biyu wanda aka kera a Canada, ya tashi ne daga Dhaka, babban birnin Bangladesh

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG